ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa, an dage taron wanda yakamata a gudanar da shi a yau Talata ne, saboda sabanin da aka samu tsakanin manya–mayan kasashen masu arzikin man kan yadda za’a yi ragin.
A halin yanzu dai kungiyar Opec tana samar da kashi 8% na man da ake haka a duniya wadanda kuma shi ne ganga miliyon 7.7 a ko wace rana.
Bayan tattaunawa ta kafafen sadarwa na bidiyo a ranar Lahadi a birnin Mosco na kasar Rasha, kasashen kungiyar ta OPEC da Rasha da sauran wadanda suke tare da su, sun dage taronne zuwa jibi don tattauna wannan batun.
Kasar Saudia da, wacce take daga cikin manya-manyan kasashen da suke da arzikin man fetur a cikin kungiyar OPEC ta bayyana cewa da wuya da amince da duk wani ragi a kasonta.
Sabani tsakanin Rasha da Saudia a farkon wannan shekara ya kai ga faduwar farashin man a kasuwannin duniya warwas, saboda cutar korona wanda ya jawo karancin bukatar man a kasuwannin duniya.
342/